1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

BOMB YA KASHE MUTANE SHIDA A IRAKI...

ZAINAB AM ABUBAKARJanuary 9, 2004
https://p.dw.com/p/Bvmf

Bayan kakkabo wani jirgin Amurka daya kashe mutane 9 dake cikinsa a jiya a garin falujja,ayau wani bomb da aka dana jikin keke ya haddasa mutuwan mutane 6 ,ayayinda ake fita daga masallaci bayan sallar jumma.Abunda ke nuni dacewa rikici na Addini ya fara kunno kai a wannan kasa da ke cikin rikici daban daban na nuna adawa da dakarun taron dangi dake cigaba da kasancewa a Irakin.

Da asubahin yaune yan yakin sari ka noke suka harba Rokoki zuwa wani Otel dake dauke da yan kasashen yammaci a birnin Bagadaza,kana daruruwan dakarun Amurka yau din sun fantsama gidajen mutane da shaguna a garin Tikrit mahaifar tsohon shugaba Sadam Hussein,da fatan kamun wadanda ake zargi da kai irin wadannan hare hare na rokoki da gurneti.

A garin Baquba mai tazarar km 65 arewacin Bagadaza,wasu yan sari ka noke sun dana wasu naurori da suka tashi a kofar masallacin yan Shitte adai dai lokacin da ake sallar jummaa,wanda kuma ya raunana akalla mutane 39,kamar yadda jamian asibiti suka sanar.

Baquba dai na mai zama daya daga cikin garuruwa da ake da yan yakin sari ka noke dake adawa da kasancewar dakarun taron dangin a wannan kasa.A lokuta da dama sojin Amurka sun kai hari aciki da kewayen garin,da nufin kama yan yakin sunkuru dake kai musu hare hare,anan ne kuma ake da mafi yawan yan Sunni.Yan shiyya dai sune kashi 60 daga cikin dari na yan Irakin million 26,amma baa basu daman fada aji a karkashin mulkin shugaba Sadam Hussein ba wanda ya kasance Sunni.Alummomin biyu sun sha fuskantar rikici dangane da sabanin raayi.

Idan baa manta ba a watan Augustan daya gabata tashin bomb a wata mota a kofar masallacin yan Shiyya a garin Najaf ya kashe mutane sama da 80.Ya zuwa yanzu dai baa gano wadanda keda hannu a wannan hari ba.

To sai dai harin rokoki da aka kaiwa Hotel din Al-hayat dake Bagadazan bai raunana kowa ba,face tagogi da suka farfashe,ayayinda tashin wani bomb da aka dasa a gefen hanya ,ya raunana wani dan Irakin da karamin yaro.

A Sumame da Dakarun Amurkan suka kai Tikrit sun kame mutane 30,bayan faduwar jirgin yakin Amurka daya kashe dukkan sojoji 9 dake ciki a garin Falujah a jiya.Koda yake Amurkawa basu fadi sanadiyyar faduwan jirgin ba,wadanda suka ganewa idanunsu sun tabbatar dacewa harbin rokoki ne ya kakkabo wannan jirgin.Wani manomi mohammed Ahmed al-jamali dake gonansa a lokacin hatsarin,yace yaga yadda rokokin da aka harban ya tsaga jirgin kafin ya kama da wuta.

To sai dai a hannu guda kuma yaune majalisar Italiya ta zartar da barin dakarunta 2,000 na karin watanni 6 a Iraki,duk da mutuwan 19 daga cikinsu da suka gamu da ajalinsu a harin bomb na mota acikin watan Nuwamban daya gabata,ayayinda ministan tsaro na Japan ya bada umurnin tura dakarun sharan fage zuwa Irakin.