Bomb ya kashe mutane 19 a Kandahar,Afganistan | Siyasa | DW | 01.06.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bomb ya kashe mutane 19 a Kandahar,Afganistan

Harin kunar bakin wake a masallacin Afganistan

default

Babban commandan rundunar yansanda na birnin Kabul na daga cikin mutane 19 da harin bomb ya ritsa dasu, a dai dai lokacin da ake sallar janaizar wani shehin malami dake adawa da yan Taliban a wani masallaci a birnin kandahar.

Jagoran rundunar yansanda na birnin Kabul Akram Khakreezwal na daga cikin wadanda suka halarci masallacin Abdul Rab Akhundzada a birnin kandahar dake tsakiyar Afganistan kuma ke fama da rikice rikice,lokacin da wannan bomb ya tarwatse,wanda ke zama karo na farko da aka kai harin boma bomai a masallaci a wannan kasa dake cigaba da kasancewa cikin halin dar dar dangane da rashin tsaro .

Rahotannin jamian yansanda na nuni dacewa wani dan kunar bakin wake ne ya afkawa wannan masallaci,ayayinda ministan harkokin cikin gida na kasar Ali Ahmad Jalali yace ya zuwa yanzu an tabbatar dacewa mutane 19 suka rigamu gidan gaskiya ayayinda wasu 52 suka jikkata.

Duk dacewa har yanzu babu wata kungiya data dauki alhakin kai wannan harin na Kandahar,sanarwar maaikatar harkokin cikin gida na Afganistan na nuni dacewa,wadanda suka kai wannan harin makiya zaman lafiya ne kuma ke gaba da addinin musulunci.

Wadanda suka samu tsira da rayukansu sun bayyana cewa dan kunar bakin waken,ya bad da kammaninsa ne cikin uniform na yansanda inda ya hade da masu tsaron commandan ruindunar yansanda,ayayinda suke shiga masalacin,domin gaisuwan taaziyyar shehk Mawlavi Abdullah Fayaz ,wanda wasu yan bindiga dadi akan babur suka bindigeshi ranar lahadi adai dai lokacin da yake barin ofishinsa.

Kafin rasuwan nasa dai Fayaz yana jagorantar majalisar malaman musulunci ,wadda gwamnatin kasar ta nada ,mutumin da kuma yasha bayyana adawansa da shugaban gwamnatin Taliban Mullah Mohammed Omar a yan kwanakin a wajejen waazi.Shekaru biyu da suka gabata dai shaihin malamin ya tsallake rijiya ta baya daga wani harin bomb da aka danganta da yan Taliban a wannan masallaci,ayayinda wannan harin daya ritsa da ransa ran lahadi,tuni yan Taliban din suka dauki alhakinsa.

Amma kakakin kungiyar yan Taliban din yace basu da masaniya a wannan harin nay au,domin babu wanda ya tuntubeshi daga cikin wakilansu.

Likitan babban asibitin Kandahar wanda yayi imanin ganin gawan dan kunar bakin wake,ya bayyanashi da kasancewa Balarabe.Banda a yan shekarun baya bayan nan dai,Afganistan bata da tarihin hare hare a masallatanta.

Kasar dai bata fuskantar gaba dake gudana tsakanin yan darikar Sunni dana shiyya kamar makwabciyarta Pakistan,inda ake yawaita kai hare hare wa masallatai.

Kandahar dai na mai kasancewa tsohon gari day an Taliban suka mamaye a baya,ayayinda harin nay au daya ritsa da rayukan 19,ke kasancewa mafi muni,a yan hare haren baya bayan nan.

 • Kwanan wata 01.06.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvbZ
 • Kwanan wata 01.06.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvbZ