1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bomb ya fashe a ofishin jakadancin Switzerland

November 2, 2010

Hukumomi a birnin Athens sun tsare mutane biyu bayan fashewar bom a ofishin jakadanci Switzerland

https://p.dw.com/p/PwIS
Hoto: Nikos Pilos

Wani bam ya fashe a ofishin jakadacin switzerland da ke birnin Athenes na kasar Girka ba tare da raunana mutun ko da guda ba. Hakazalika Jami'an 'yan sandan kasar ta Girka sun yi nasarar tarwatsa sakon da ke kunshe da bam da aka aike zuwa ga ofishin jakadancin Bulgariya. Tun a jiya litinin ne dai jami'an na athenes suka fara bankado yunkurin kaddamar da hare-hare akan ofisoshin jakadancin wasu kasashe da kuma shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa. Ya zuwa yanzu dai 'yan sanda sun tsare mutane biyu tun bayan fashewar daya daga cikin sakwanin da suka aika, da ya kona daya daga cikin ma'aikatar gidan waya. Jami'an tasro na ci gaba da binciken Kullin bama-bamai da aka aike ofisoshin jakadancin Mexico da Beljium da kuma Netherland. Shekarun wadanda ake zargi da wannan aika-aikan na birnin athenes bai fi 24 ba. Hukumomin Athenes sun yi ammanar cewar mambobin kungiyar masu tasananin ra'ayi ne suka yi wannan yunkuri.

Mawallafi : Mouhammad Awal Balarabe

Edita : Abdullahi Tanko Bala