Bomb din sojin Amurka ya kashe yansandan Afganistan 12 | Labarai | DW | 17.08.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bomb din sojin Amurka ya kashe yansandan Afganistan 12

Yansandan gudanar da sintiri kann iyakar Afganistan ta kudanci guda 12 suka rasa rayukansu,lokacinda wani bomb ya fado daga jirgin yaki mallakar dakarun Amurka,ayayinda wasu jamian yansandan biyu suka jikkata.Gwamnan gunduwar Akram Akhpul Wak,ya fadawa kamfanin dillancin labaru na Reuters cewa wannan hadari ya auku ne a garin Paktika,dake kann iyakokin Afganistan da Pakistan.Kakakin Rundunar Sojin Amurka ya bayyana cewa ana gudanar da bincike a dangane da wannan rahoto.Dakarun na Amurka dai suke da alhakin tabbatar da tsaro a garin na paktika.Ayau dinne kuma wani dan kunar bakin wake ya tayar da bomb dayake dauke dashi a kusa da ofishin yansanda a garin Uruzgan dake kudancin Afganistan,inda ya raunana jamian yansanda 7.Bugu da kari tashin wani bomb da aka dasa a gefen hanya ya raunan wani jamiin sojin kawance a gunduwar Kanndahar.Wadannan hare hare dai na masu zama na baya bayannnan a irin tashe tashen hankula da kasar ta Afganistan ke fuskanta.

 • Kwanan wata 17.08.2006
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5s
 • Kwanan wata 17.08.2006
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5s