1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bom yayi ajalin mutane 19 a Iraqi

May 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuKZ

Wani dan kunar bakin wake ya tashi wani bom a cikin wata karamar mota a tsakiyar Bagadaza dake Iraqi. Hakan yayi ajalin mutane 19 nan take tare da jikkata wasu 46.Tuni dai akayi gaba da wadanda suka jikkatan izuwa asibiti.Al´amarin dai ya faru ne a lokacin da jakadun Amurka da Iran ke ganawa, kann al´amurran rashin tsaro dake ci gaba da tabarbarewa a Iraqin.