Bom ya tashi a Bandung na kasar Indonesiya | Labarai | DW | 27.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bom ya tashi a Bandung na kasar Indonesiya

'Yan sandan kasar Indonesiya sun tabbatar da tashin Bom a wani yanki na kasar.

Rahotanni daga Jakarta babban birnin kasar Indonesiya, na cewa wani bom ya tashi a wani wajen da ake kira Bandung, inda jami'an 'yan sandan kasar suka ce sun kama tare da raunata wanda ya kai harin da safiyar wanna Litinin. Jami'an suka ce mutumin ya kai harin a wata ma'aikatar gwamnati da ke Bandung din kan babur, ya kuma ajiye wata tukunyar gas, inda ba da jimawa ba ne tukunyar ta tashi.

Sun kuma tabbatar da aikewa da kwararrun masu kwance boma-bomai a yankin don ci gaba da binciken yiwuwar samun wani abu da ke da hadari. Babu dai wani da ya rasa ransa sakamakon harin, Sai dai jami'an tsaron sun danganta harin da yunkurin tilasta sakin wasu fursunoni da ake tsare da su.