1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bom ya halaka mutane a Somaliya

Wani bom da ya tashi cikin wata mota ya halaka mutane a babban birnin Somaliya.

Gidan abinci da Bom ya tarwatsa

Gidan abinci da Bom ya tarwatsa a Mogadishu

Rahotanni daga Mogadishu babban birnin Somalia, na cewa akalla mutane 20 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka ji raunuka sakamakon tashin bom a wata kasuwar da ke a birnin. Bom din da ya tashi cikin wata mota da ke tsaye a gefen wani gidan cin abinci, ya tashi ne yayin da ake tsakiyar hada-hada a kasuwar.

Wani da ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma ke dauke da raunukan da ya ji daga tashin bom din, ya ce wani ne ya ajiye motar, inda jim kadan da barin sa wajen sai ya tayar da bom din da ke a ciki. Wannan harin wanda mahukuntan kasar ta Somalia suka tabbatar da aukuwarsa dai shi ne na farko bayan zaben Shugaban kasar Mohammad Abdullahi a ranar 8 ga wannan wata na Fabrairu, wanda tuni ya yi Allah wadai da harin.

Gabanin kaddamar da harin ma dai kungiyar Al Shabbab da ta yi kaurin suna wajen kai hare-hare a kasar da ma makwabta ta yi alkwarin gigita sabuwar gwamnatin kasar.