1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta yi barazanar hana zabe a Najeriya

February 18, 2015

Hare-haren kunar bakin wake da kuma fada mai tsanani da suka wakana a ranar Talata a Tarayyar Najeriya sun yi sanadiyar rasuwar mutane a kalla 40 kasa da makonni shidda kafin zabubukan kasar.

https://p.dw.com/p/1EdXe
Hoto: picture alliance/AP Photo

Da yake magana ta wani sabon bidiyo da ya fitar kamar yadda ya saba, shugaban kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau ya ce, ko sun mutu ko suna raye, baza'a gudanar da wannan zabe ba, domin a cewarsa Allah ma bai zai bada dama a yi zaben ba. A yammacin ranar Talata (17.02.2015) dai an yi wani kazamin fada bisa hanyar Maiduguri tsakanin 'yan kungiyar da dakarun kasar Chadi, inda a cewar dakarun na Chadi sojojinsu biyu sun rasu, yayin da su kuma suka kashe dumbun 'yan kungiyar ta Boko Haram a nisan km 90 da babban birnin jihar ta Borno. Kuma da fako a wannan rana wasu hare-hare sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 30 a garin Yamakurmi da ke a nisan km hudu da garin Biu da ke arewa maso gabashin kasar.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu