Boko Haram ta kashe manoma a Najeriya | Labarai | DW | 08.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta kashe manoma a Najeriya

Wasu 'yan bindiga ne da ke tafe cikin motar daukar kaya sanfurin pick-up da baburan hawa suka kai harin a wajen birnin Maiduguri da ke jihar Borno a tarayyar Najeriya.

Mayakan Boko Haram sun halaka mutane takwas a wasu yankuna da al'ummarsu ke zama mafi rinjaye manoma a Arewa maso Gabashin Najeriya kamar yadda 'yan kungiyar kato da gora da mazauna yankunan suka fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP a wannan rana ta Juma'a.

Harin da aka kai wasu 'yan bindiga ne da ke tafe cikin motar daukar kaya sanfurin pick-up da baburan hawa suka kai shi a wajen birnin Maiduguri a ranakun Laraba da Alhamis.

Sun kuma kwace wa al'umma kayan abinci baya da sa wuta a kauyika uku da wasu a runbunan ajiyar kayan abincin, lamarin da ya sanya mutane suka gudu a cewar Ibrahim Liman shugaban sojan sakan na 'yan kato da gora.