Boko Haram ta kai hari a Kamaru
August 25, 2017Talla
Mayakan na Boko Haram sun kaddamar da harin ne a cikin daren da ya gabata a kauyen Gakara da ke a kan iyakar Kamarun da Najeriya, bayanai daga bakin mazauna yankin da lamarin ya faru na cewa maharan sun kona gidaje kimanin 30 a wannan harin.
Majiya daga ma'aikatar tsaron kasar na cewa mayakan da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne sun halaka mutane goma sha daya a harin tare da yin garkuwa da wasu mutane takwas harin da suka kai a yankin arewacin kasar.