1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta kai farmaki makarantar 'yan mata

Yusuf Bala Nayaya MNA
February 20, 2018

Masu ikirarin jihadin na Boko Haram sun kai farmaki makarantar 'yan mata a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya lamarin da ya haifar da fargaba.

https://p.dw.com/p/2sxqO
Boko Haram
An dai shiga kwan gaba kwan baya kan matsalar ta Boko Haram a NajeriyarHoto: Java

Mayakan da suka ja wata tawaga cikin motoci samfurin akori kura ta daukar kaya sun isa kauyen Dapchi a yankin Bursari na jihar Yobe da misalin karfe shida na yammaci inda suka tunkari makarantar kamar yadda Sheriff Aisami wani da ya sheda lamarin ya fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Aisami ya ce da saukar mayakan a garin sun rika harbe-harbe da fasa wasu abubuwa masu kara, wannan ya ja hankalin 'yan makarantar ta 'yan mata da ke garin inda daliban da malamansu suka ranta cikin na kare kafin mayakan su karasa makarantar. 'Yan kungiyar dai ta Boko Haram sun sace kayayyaki da suke bukata a makarantar.