1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Harin kunar bakin wake a konduga

Salissou Boukari
May 15, 2018

Wani harin kunar bakin wake da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, ya yi sanadiyyar mutuwar wasu 'yan kato da gora guda biyar a wani wurin bincike na jami'an tsaro.

https://p.dw.com/p/2xm2t
Nigeria Konduga Selbstmord-Attentat
Hoto: Getty Images/AFP

Harin ya wakana ne a wannan Talatar a wani wurin bincike da ke mafitar birnin Konduga mai nisan kilo mita 35 da Maiduguri babban birnin jihar Borno. Wasu mutanen guda biyar kuma sun samu raunuka bayan da dan kunar bakin waken ya tarwatsa kan shi a cewar Abdukadir Ibrahim mai magana da yawun hukumar agaji ta NEMA a tarayyar ta Najeriya.

Kimanin makonni biyu da suka gabata ma dai, wasu tagwayen hare-haren da aka kai a cikin wani masallaci a jihar Adamawa, sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 86 yayin da wasu da dama kuma suka samu raunuka. Tun dai daga shekara ta 2009 ce kungiyar Boko Haram ke aikata ta'asa a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.