1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta halaka mutane da kona gari

Kisan da banka wuta a kauyika na zuwa adaidai lokacin da ake cewa an tasamma karar da Boko Haram a Najeriya. Abin da ke sanya shakku a zukata na al'umma.

Mayakan Boko Haram sun afka wasu kauyika uku a Arewa maso Gabashin na Najeriya inda suka halaka mutane biyar tare da sanya wa kauyikan wuta kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyana a ranar Alhamis.

Su dai mayakan a ranar Laraba sun afka kauyukan Huyum da Sabongarin Huyum da Wasada akan baburan hawa inda a nan ne suka kashe mutanen kafin daga bisani su sanya wuta a gidaje da gonaki kamar yadda wadanda suka sheda lamarin suka bayyana.

A cewar wani Bala Jonah mazaunin garin na Huyum mayakan sun yi garkuwa da su kafin su kashe wasu daga cikinsu inda kuma suka kone abin da su ka noma su na daf da yin girbi.Tuni dai daruruwa na mutanen suka yi kaura zuwa wasu kauyika makota.