1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram na ci gaba da wanzuwa a Borno

Al-Amin Suleiman MohammadMarch 31, 2016

Ministan tsaron Najeriya ya ce Boko Haram na iko da wasu kananan hukumomi biyu na jihar Borno, duk da irin nasarar da sojojin kasar ke samu.

https://p.dw.com/p/1INLu
Nigeria Armee Soldaten
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Ikechukwu

Al'ummar yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun fara tofa albarakcin bakinsu, bayan da ministan tsaro na Najeriya ya bayyana cewa kungiyar Boko Haram na ci gaba da gudanar da ayyukanta a kananan hukumomi biyu na jihar Borno duk da irin nasarar da ake samu kansu.

Ministan tsaro na Najeriya Mansur Dan-Ali ya bayyana a wata kafar yada labarai cewa akwai kananan hukumomi guda biyu da yanzu haka suka saura a hannun ikon mayakan Boko Haram. Duk da dai cewa ofishin ministan ya fito daga baya ya nuna cewa ba daukacin kananan hukumomin ne ke karkashin ikon Boko Haram ba, suna nan ne dai jifa-jifa a wuraren. Yawancin al'ummar shiyyar sun fahimci cewa akwai sauran aiki a wannan yaki.

Da sauran aiki gaban sojojin Najeriya

Yawancin dai mazauna yankin na Arewa maso Gabashin Najeriya dai sun nuna cewa duk da an samu nasara a wasu wurare amma akwai sauran yankuna da ake fama da kalubalen tsaron wanda ya fi yadda ministan ya zayyana.

Bewaffnete Bewohner Patrouille Boko Haram Nigeria Chibok
Kungiyoyin 'yan Kato da gora suna ba da ta su gundunmawa a yakin da ake yi da Boko HaramHoto: picture-alliance/AP Photo/S.Alamba

Wani mazaunin yankin da bai so a bayyana sunansa ba ya shaida wa wakilinmu Al-Amin Suleiman Mohammad ta wayar tarho cewa "akwai manyan garuruwa a tabkin Chadi da har yanzu babu sojojin Najeriya a ciki, abin da ka iya haifar da koma baya a nasarorin da ake cimmawa."

Talakawan wannan yankin sun amince da cewa bayanai da mutanen yankin ke bayyanawa shi ne abin dogaro, sabanin bayanai da hukumomi suke fitarwa da sau tari na kin nuna gazawa ne. Malam Bala Kali na cikin masu irin wannan fahimta.

"Abin da mutanen yankin ke fadi shi ne gaskiya domin ita gwamnati ba za ta fito ta nuna gazawarta a fili ba. Kokari take ta kare muradunta. Amma hakika akwai lauje cikin nadi."

Honorable Adamu Musa Dan Amar na ganin akwai daurewar kai dangane da yadda ake samun sabanin bayanai kan nasarorin da ake cimmawa a wannan yaki.

"Su ma mutanen wurin ba dole a yadda da maganganus ba, domin ba kowa ne ke son a ci nasara ba. Wani bukatarsa kawai ya sa gaba. Saboda haka ba za mu iya gane gaskiyar wannan baki biyu da ake samu ba."

Rudani kan bayanan nasarorin da ake samu

Wasu mazauna yankin kamar Alhaji Abubakar Gamandi na ganin ana cimma nasara gagaruma sabanin yadda ake bayyana nasarorin baya.

Nigeria Abuja Präsident Muhammadu Buhari
Shugaba Buhari: "Babu sauran ko da gari daya da ke hannun Boko Haram."Hoto: picture-alliance/dpa/W. Krumm

A baya ma dai an samu rudani bayanai da wani Sanata mai wakiltar jihar Borno ya bayyana cewa akwai yankuna da har yanzu ke karkashin ikon mayakan Boko Haram lamarin da gwamnatin jihar Borno ta musa. Shi ma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha fitowa a 'yan makonni da suka shude yana bayyana cewa babu sauran ko da gari daya da ke karkashin ikon mayakan Boko Haram.

To ko ina ake samun wannan matsala ta sabanin bayanai? Abubakar Baba Abdullahi wani mai sharhi kan harkokin yau da kullum a Najeriya ya ce.

"Matsala na nan tsakanin shugabanni da jami'an sojoji. Soja shi ne yake yaki da 'yan Boko Haram, shi ya fadi magana daban, shi kuma shugaban kasa a tunaninsa an cin karfin Boko Haram. Mutanen yankin kuma suna zaman dar-dar domin har yanzu suna ganin mayakan Boko Haram suna shawagi a yankin. To da matsala a nan."

Duk da hare-hare jifa-jifa da ake samu na bindiga da na kunar bakin wake a yankunan Arewa maso Gabashin Najeriya musamnan kan iyokokinta da kasashen Nijar da Chadi da Kamaru, ministan tsaron na Najeriya ya ce nan da watanni biyu za a ci galabar wannan yaki da ake yi.