Blair zai gabatar da sabbin shawarwarin samar da zaman lafiya a GTT | Labarai | DW | 28.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Blair zai gabatar da sabbin shawarwarin samar da zaman lafiya a GTT

Tsohon FM Birtaniya Tony Blair ya ce ya na niyar tsara wasu kwararan shawarwari ga zaman lafiyar yankin GTT nan da watanni kadan masu zuwa. Wannan sanarwa ta zo ne a daidai lokacin da Blair yake ganawa da wakilan bangarorin hudu da suka hada da KTT, MDD, Amirka da Rasha sai kuma wasu kasashen yankina na GTT. Blair dai ba dade da dawowa daga yankin ba inda ya kai ziyarar ta farko ta farko tun bayan nada a matsayin wakili na musamman na bangarorin 4 dake tattauna batun samar da zaman lafiya a GTT. Blair ya bayyana tattaunawar da yayi da shugabannin Isra´ila da Falasdinu a farko wannan mako da cewa wata dama ta samu a wannan lokaci.