Blair ya yi kira ga kasashen Larabawa da su tinkari kalubale daga Iran | Labarai | DW | 20.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Blair ya yi kira ga kasashen Larabawa da su tinkari kalubale daga Iran

FM Birtaniya Tony Blair ya yi kira ga kasashen musulmi masu sassaucin ra´ayi da su kafa abin da ya kira kawance na ´yan sassauci don tinkarar kalubalen da ake fuskanta daga Iran. Lokacin da yake jawabi a Dubai a karshen rangadin kasashen yankin GTT Blair ya bayyana yakin da ake yi da akidojin masu tsattsauran ra´ayi da cewa shi ne kalubalen da ake fuskanta a wannan karni na 21.