1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Blair ya yaba da kiran zabe da shugaban Palasdinawa yayi

December 18, 2006
https://p.dw.com/p/BuXM

Firaminstan Burtaniya Tony Blair ya yaba da kiran zabe da shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas yayi yana mai cewa makonni na gaba masu zuwa suna da muhimmanci ga makomar yankin.

Blair yana magana ne wajen wata ganawa da manema labarai bayan tattaunawarsu da Abbas a birnin Ramallah dake yamma da gabara kogn Jordan.

Tony Blair wanda ke rangadin yankin a kokarinsa na farfado da shiryukan zaman lafiya a yankin,nan gaba zai tattauna da Firamistan Israila Ehud Olmert a birnin Qudus.

A halinda ake ciki kuma,bangarorin adawa a yankin na Palasdinawa sunyi musayar wuta kusa da ofishin maaikatar harkokin wajen yankin a Gaza.

Mai magana da yawun dakarun Hamas yace anyi musayar wutan ne tsakanin magoya bayan Abbas da kuma yan sanda dake gadin maaikatar.

Fada ya barke ne ranar asabar bayan kira da shugaba Mahmud Abbas yayi na sake gudanar zaben shugaban kasa da na yan majalisa,batu da kungiyar Hamas tace wani yunkuri ne nayi mata juyin mulki.