1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Blair ya kai ziyara ban kwana ta ba zata a Irak

May 19, 2007
https://p.dw.com/p/BuLB

Praministan Britania Tony Blair, ya kai ziyara bankwana ta ba zata, a ƙasar Irak, inda ya gana da takwaran sa, Nuri Al-Maliki, da kuma shugaban ƙasa, Jalal Talabani.

Tony Blair, yayi anfani da wannan dama, domin jaddada goyan bayan Britania, a game da ayyukan samar da zaman lahai a ƙasar Irak.

Jim kaɗan kamin saukar Blair birnin Bagadaza, yan ƙunar bakin waƙe ,sun kai sabin hare-hare kann sojojin Amurika, wanda take !!! 8 daga cikin su suka sheƙa lahira.

Rikicin Irak, na daga sahun matsalolin da su ka hadasawa Tony Blair baƙin jinni, a kasar Britania, wanda a sakamakon hakan, cilas, ya bayyana yin murabus daga muƙamnin sa, ranar 27 ga wata mai kamawa.

Saidai a ganawar da yayi da hukumomin Irak, ya tabbatar masu da cewa, bai yi cizon yatsa ba, a game da hunkunci da ya yanken na aika sojoji a Irak.