1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Blair ya ja hankalin kasashen turai su cika alkawarin su Nahiyar Afrika

April 25, 2007
https://p.dw.com/p/Btve
Alkawarin kasashen G8 ga Nahiyar Afrika
Alkawarin kasashen G8 ga Nahiyar AfrikaHoto: AP

P/M Britaniya Tony Blair ya yi kashedin cewa akwai gagarumin kalubale a gaban kasashen yammacin turai idan suka ki cika alkawuran da suka yi na taimakawa kasashen Afrika fita daga kangin talauci. Tony Blair ya yi wannan kashedin ne a wani taro a birnin Berlin wanda ya hada da tsohon sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel domin nazarin aikin kwamitin kwararu kan cigaban nahiyar Afrika.

Shi dai wannan kwamiti wanda aka kafa shi a watan Yuni na shekarar bara, a karkashin jagorancin tsohon sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan, manufar sa shi ne bin kadin cigaban da aka samu a alkawuran da manyan kasashe masu arziki na duniya suka yi na bada tallafi domin taimakawa cigaban nahiyar Afrika.

Shekaru biyu da suka wuce kungiyar kasashe masu cigaban masanaántu na duniya wato G8 a babban taron da suka gudanar a Gleaneagles ta kasar Scotland bisa jagorancin Britaniya, suka yi alkawarin yafe kaso mai tsoka na bashin da suke bin kasashen Afrika tare kuma da rubanya gudunmawar jin kai ga nahiyar ta Afrika ya zuwa shekara ta 2010.

Ko da yake kasashen na G8 sun yi kokari wajen yafewa Afrikan basuka da dama da yawan su ya kai dala miliyan dubu 38, a daya bangaren kuwa har yanzu da sauran tafiya a alkawarin da suka yi na rubanya taimakon raya kasa ga kasashen Afrika. P/M Tony Blair yace rashin cika alkawarin ka iya haifar da sakamako mawuyaci ga kasashen turai. Yace idan na dubi irin abin dake faruwa a Afrika musamman a wasu yankuna da ake fama da munanan matsaloli kamar Sudan da Somalia da sauran su, na kan ji cewa idan bamu yi kyakyawan nazarin nahiyar ta Afrika da kuma bukatar ta, ta raya kasa da samun cigaba mai maána, to babu shakka za mu wayi gari bisa son zuciya, mu sami kan mu an yiwa kasashe kamar Jamus da Britaniya taádi sakamakon talauci da rigingimu da kwararar yan gudun hijira masu yawa da kuma karuwar yan taáda.

Balair ya kara da cewa akwai banbanci na zahiri a wurare wadanda aka sami taimakon raya kasa. Alal misali harkokin su na lafiya dana ilmi sun sami inganta a sakamakon tallafi daga da kwakwarar kudiri daga alúmomin kasa da kasa.

Ita kuwa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ci alwashin cewa batun na Afrika zai kasance a kan gaba a jadawalin taron kungiyar ta G8 da zaá gudanar a bana karkashin jagorancin kaasar Jamus. Ta ce zata tabbatar da ganin an cigaba da kai gunmawar jin kai ga kasashe matalauta ba tare da katsewa ba. Tana mai cewa za su dora a inda taron na Gleaneagles ya tsaya.

Shima tsohon sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan kuma shugaban kwamitin sa ido kan tabbatar da cika alkawarin da kasashen masu cigaban masanaántu suka yiwa nahiyar ta Afrika yace kwamitin ba yana neman wasu sabbin alkawura bane, sai dai cika wadanda aka dauka tun da farko. Yace idan na dubi ayyuka masu ban shaáwa a kasashen tarayyar Turai a yau, ya kan bani kwarin gwiwa. A yau na yi imanin cewa yaki a halin da ake cikibama zaka yi tunanin aukuwar yaki a kasashen turai ba, amma kuma wannan nahiya ce wadda ta ga yakin duniya har guda biyu, saboda haka nake fata yayn mu da jikokin mu suma za su wayi gari su ce yaki a Afrika ya zama tarihi. Kofi Annan na mai tsokaci da rigingimu a kasashen Angola da Saliyo da Liberia da Burundi da Eritrea da kuma Habasha. Yace shugabanin Afrika suna da masaniya cewa akwai bukatar su sulhunta wadannan matsaloli na siyasa domin samun sukunin maida hankali kan cigaban tattalin arziki da walwalar jamaá.