1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Blair ya baiyana goyon baya ga magajin sa

May 2, 2007
https://p.dw.com/p/BuMQ

P/M Britaniya Tony Blair ya bada cikakken goyon baya ga Ministan kudi Gordon Brown a matsayin wanda zai gaje shi, yana mai cewa zai sanar da lokacin da zai ajiye aiki bayan shafe shekaru goma a karagar mulki. Blair wanda a tsawon lokaci ya ki baiyana magajin na sa, yace ministan kudin Gordon Brown zai kasance P/M na kwarai. Blair da Gordon Brown sun kasance aminan juna tun lokacin da suke majalisar dokoki a shekarar 1983. Dangantakar su ta yi tsammi musamman a lokacin da Gordon Brown ya rika hasashen cewa Blair ya saba alkawari mika ragamar mulki kamar yadda aka tsara.