1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Blair ya amsa tambayoyi a gaban ´yan sandan Birtaniya

´Yan sandan Birtaniya sun yiwa FM Tony Blair tambayoyi a binciken da suke yi na ko jam´iyar Labour ta karbi makudan kudade don ba da lambobi girmamawa na kasa. Wani kakakin gwamnati ya ce an yiwa Blair tambayoyi a matsayi shaida amma ba matsayin wanda ake tuhuma da aikata laifi ba. kawo yanzu an yiwa mutane kimanin 90 tambayoyi, bayan da ya fito fili cewa an bawa jam´iyar Labour rance a boye gabanin zabukan da aka gudanar a bara. A cikin watan gobe ake sa ran hukumar ´yan sanda ta Scotland Yard zata ba da sakamakon binciken.