Blair na kara shan matsin lamba daga ´ya´yan jam´iyarsa | Labarai | DW | 06.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Blair na kara shan matsin lamba daga ´ya´yan jam´iyarsa

FM Birtaniya Tony Blair na kara shan matsin lamba bayan da jam´iyar sa ta Labour ta sha mummunan kaye a zabukan kananan hukumomi. Kafofin yada labaru sun rawaito cewar ´ya´yan jam´iyar a majalisar dokoki sun rubuta wata takarda wadda a ciki suka bukaci Tony Blair ya nuna musu ranar da zai mika mukamin sa ga sakataren kudi Gordon Brown. A zabukan da aka gudanar a ranar alhamis, jam´iyar Labour ta yi rasa kujeru sama da 300 na kananan hukumomi. Ta samu kashi 26 cikin 100 na yawan kuri´un da aka kada, wato ita ta zo ta biyu bayan jama´iyar Conservative ta ´yan ra´ayin mazan jiya, sannan jam´iyar Liberal Democrats ta zo ta 3. sakamakon wannan kaye da jam´iyarsa ta sha, FM Blair yayiwa gwamnatinsa garambawul, inda ya sauke sakataren harkokin waje Jack Straw daga mukaminsa sannan ya sallami sakataren cikin gida Charles Clarke. Yanzu sakatariyar kare muhalli Margaret Becket zata maye gurbin Straw, inda zata zama mace ta farko da ta taba rike wannan mukami a Birtaniya.