1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

BJP ta lashe zaɓen jihar Gujurat

Jamiiyyar Adawa ta mabiya addinin Hindu dake kasar India Watau BJP,ta lashe zaɓen jihar Gujurat ,dake fama da rigingimu na banbancin addini.Wannan zabe na mai kasancewar wani mizani ne na gwajin irin tasirin da jamiiyyar zatayai a zaben kasa baki daya.Bayan kamma kidayan kuriu a zaben na wannan jiha dake yammacin India,hukumar zabe tace jamiiyyar BJP ta samu kujeru 117 daga cikin majalisar jihar mai wakilai 182.Ayayinda jamiiyyar Congress dake mulkin hadaka a kasar,ta samu kujeru 59,kana sauran kananan jamiiyyu suka raba sauran kujeru 6 dake majalisar.Wannan shine karo na hudu da jammiiyyar yan Hindu ke lashe zabe a Gujurat,akarkashin jagorancin minista mai tsattsauran raayi Narendra Modi.