1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bitar shekara ta abubuwan da suka faru

Ubale Musa/AHDecember 31, 2015

Misali a Najeriya Babban abin da ya fi ɗaukar hankali a wannan shekara ta 2015 da ke shirin kammala, shi ne zuwa Muhammad Buhari kan karagar mulki.

https://p.dw.com/p/1HWWE
Nigeria - Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa

Sabon shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sha rantsuwar kamun aiki a ranar 29 ga watan Mayun da ya shuɗe a wani abin da ke zaman ƙoƙari na kafun tarihi na siyasa cikin ƙasar.Dan shekaru 73 Buharin dai yai nasarar karɓe goruba a hannun kuturu a cikin mulki dama siyasar ƙasar dake nuna alamun rikiɗewa ya zuwa tsarin mai ƙarfi sai Allah.