Bisa ga dukkan alamu Nazarbayev ya lashe zaben shugaban kasar Kazakhstan | Labarai | DW | 04.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bisa ga dukkan alamu Nazarbayev ya lashe zaben shugaban kasar Kazakhstan

Shugaban Kazakhstan Nursultan Nazarbayev ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar yau da gagarumin rinjaye. Hasashen da aka yi bayan kammala kada kuri´u, ya nunar da cewa shugaba Nazarbayev ya samu kimanin kashi 85 cikin 100 na yawan kuri´un da aka kada., yayin da shugaban ´yan adawa Zarmakan Tuyakbai ya samu kashi 10 cikin 100. ´Yan adawa dai sun zargi shugaba Nazarbayev da tabka magudin zabe, cin hanci da rashawa tare da tafiyar da mulki irin na kama karya. Idan aka tabbatar da wannan nasarar, to shugaban zai yi wani sabon wa´adin shekaru 7 akan mulki, bayan ya shafe shekaru 16 yana jan ragamar shugabancin kasar. ´Yan kasashen yamma, wadanda suka kula da yadda zaben ya gudana sun ce ba´a taba kamanta gaskiya da adalci a zabukan da ake yi a kasar ta Kazakhstan mai arzikin man fetir ba.