Bisa ga dukkan alamu an yi garkuwa da wani Bajamushe a Afghanistan | Labarai | DW | 04.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bisa ga dukkan alamu an yi garkuwa da wani Bajamushe a Afghanistan

Wata majiya ta ma´aikatar harkokin wajen Jamus ta yi nuni da cewa an yi garkuwa da wani dan kasar ta a Afghanistan. Kakakin ma´aikatar waje Martin Jäger ya ce Bajamushen ya bace ne tun a ranar alhamis da ta gabata kuma hukumomi sun yi imani cewar sace shi aka yi. Kakakin ya ce mutumin ba sojin Jamus ba ne, ba dan jarida ba ne kana kuma ba ma´aikacin wata kungiyar agaji ba ne. Kawo yanzu dai ba´a ba da karin bayani ba.