1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birtaniya za ta mika Al-Masri ga Amirka

Wata kotu a Biritaniya ta yanke hukuncin miƙa mai tsattsauran ra´ayin nan, wato Abu Hamza al-Masri ga ƙasar Amirka. Kotun ta ce Al-Masri zai fuskanci cajin da ake masane kann ayyukan ta´addanci a ƙasar ta Amirka ne.Abu Hamza, wanda haifaffen ƙasar Masar ne, na zaman waƙafi a ƙasar ta Biritaniya ne na tsawon shekaru bakwai. An yanke masa wannan hukuncinne, sakamakon tunzura magoya bayan sa, gudanar da ayyukan kisan kai ga kafirai.A yanzu haka dai Amirkan na zargin Abu Hamza da laifuffuka 11, dake da jibinta da ayyukan ta´addanci. Kafin dai Miƙa Abu Hamza ga mahukuntan na Amirka, dole ne a samu amincewar sakataren harkokin cikin gida na ƙasar ta Biritaniya.