Birtaniya za ta karawa Najeriya kudaden agaji
August 31, 2017Talla
Itama ana ta banagaren sakatariyar raya kasashe ta Birtaniya Priti Patel, da take bayyana aniyar kasar a kan kudaden agajin a yayin da suka ziyarci yankunan da ta'addancin Boko Haram din ya shafa a jihohin da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, ta ce za'a raba Kudaden tallafin ne a cikin shekaru hudu nan gaba.
A yanzu dai sama da mutane miliyan guda ne ke fuskantar barazanar yunwa a Najeriya sakamakon rashin tasirin noma, amma suna da yakinin wadannan tallafi ka iya farfado da harkokin more rayuwa da zai ingata fannin kiwo lafiya da Ialimi.