1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya za ta bukaci gaggauta sauye-sauye cikin EU

Mohammad Nasiru AwalJune 20, 2016

Ana kankan tsakanin masu so da masu kin ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai a kuri'ar raba gardama da 'yan kasar za su kada.

https://p.dw.com/p/1JA5a
Philip Hammond Außenminister Großbritannien
Philip Hammond sakataren harkokin wajen BirtaniyaHoto: Getty Images/AFP/N. Halle'n

Gwammatin Birtaniya ta ce idan kasar ta zabi cigaba da zama cikin kungiyar Tarayyar Turai EU, to za ta yi kira da a gaggauta yi wa kungiyar canje-canje. A lokacin da yake magana a gun taron ministocin harkokin wajen kasashen EU a Luxemburg, sakataren harkokin wajen Birtaniya Philip Hammond ya ce dole a gaggauta aiwatar da alkawuran da shugabannin EU suka dauka a cikin watan Fabrairu da ya gabata. A lokaci daya kuma ya yi gargadin cewa zaben raba gardamar ta ranar Alhamis mai zuwa mataki ne da ba za a iya canjawa ba.

Ya ce: "Ana kankankan a batun kuri'ar raba gardamar, amma ko yaya za ta kaya dai sakonmu ga al'ummar Birtaniya shi ne shawara ce da ba za a iya canjawa ba, idan Birtaniya ta yanke shawarar ficewa to ke nan bakin alkalami ya bushe, Birtaniya ba za ta iya sake komawa cikin EU ba face a kan ka'idoji da ba za a taba amincewa da su ba, wato kamar kasancewa cikin kasashe masu amfani da kudin Euro da yarjejaniyar Schengen da dai sauransu."