1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya za ta bayar da tallafi ga Somaliya

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 15, 2017

Sakataren harkokin kasashen ketare na Birtaniya Boris Johnson ya bayyana cewa, Birtaniya za ta bayar da taimako ga kasar Somaliya na makudan kudade domin shawo kan matsalar fari da kasar ke fama da shi.

https://p.dw.com/p/2ZFuk
Matsalar fari a Somaliya: Birtaniya za ta taimaka
Matsalar fari a Somaliya: Birtaniya za ta taimakaHoto: picture alliance/AP Photo/F. Abdi Warsameh

Johnson ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da sabon shugaban kasar Somaliyan Mohamed Abdullahi Mohamed yayin wata ziyarar ba zata da ya kai Mogadishu babban birnin kasar. Johnson wanda ya ce Birtaniya za ta taimaki Somaliyan da makudan kudi da yawansu ya kai Pam miliyan 110 a matsayin agaji ga dinbin al'ummar da ke tsananin bukatar taimako a kasar, inda ya ce:

"Fari da makamantansa kan afku sakamakon sakaci irin na mahukuntan al'umma, misali sakaci daga bangaren gwamnati da kuma cin hanci. A shirye muke mu taimaka muku a gwagwarmayar da kuke na yakar 'yan ta'adda. Muna alfahari wajen taimakon ku a wannan fanni.