1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta rufe ofishin jakadancinta a birnin Amman

January 7, 2006
https://p.dw.com/p/BvDL

Birtaniya ta rufe ofishin jakadancin ta a Jordan saboda fargabar kai hare haren ta´addanci akan ´yan kasashen yamma dake wannan kasa. Wannan matakin ya zo ne watanni biyu bayan hare haren kunar bakin har guda 3 da aka kai kan wasu manyan otel otel a birnin Amman wanda ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 50. Kungiyar al-Qaida a Iraqi karkashin jagorancin dan Jordan Abu Musab Al-Zarqawi ta yi ikirarin kai wadannan hare haren. Ma´aikatar harkokin wajen Birtaniya ta sanar da rufe ofishin jakadancin a cikin watan sanarwa da ta buga a shafinta na intanat. Ma´aikatar harkokin wajen ta ce ta samu gamsassun rahotanni da ke nuni da cewa ´yan ta´adda na shirye shiryen karshe na kai hare hare akan ´yan yamma da kuma wuraren da turawan yamma kai yawaita ziyara a cikin Jordan. Sanarwar ta ce ofishin jakandancin zai ci-gaba da zama a rufe har zuwa wani lokaci da ba´a fayyace ba.