1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta mika takardar barin EU

Yusuf Bala Nayaya
March 29, 2017

Tim Barrow, jakadan Birtaniya a Kungiyar EU shi ya mika wannan takarda ga Donald Tusk Shugaban Kungiyar EU.

https://p.dw.com/p/2aEU2
EU Großbritannien Brexit Brief Botschafter Barrow mit Tusk
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Herman

Birtaniya a hukumance ta mika takardar shirin barin Kungiyar Tarayyar Turai EU a wannan rana ta Laraba, inda aka mika takardar barin wannan kungiya ga Shugaban Kungiyar ta EU Donald Tusk kamar yadda Firaminista Theresa May ta bayyana a gaban majalisa:

"Babban jakadan Birtaniya zuwa ga Kungiyar EU a madadina ya mika matsayar gwamnatin Birtaniya abin da zai motsa yarjejeniyar Kungiyar EU mai lamba 50. Lamarin da ke nuna cewa al'ummar Birtaniya sun daura damba ta aiwatar da aniyarsu ta barin Kungiyar ta EU."

Tim Barrow, jakadan Birtaniya a Kungiyar ta EU shi ya mika wannan takardar ta fara shirin fita daga EU wacce Firaminista Theresa May ta rattabawa hannu a kanta, ya kuma mikata ne ga Tusk a ofishinsa da ke birnin Brussels.

Da ta ke mayar da nasu martani kan ficewar ta Birtaniya daga EU Ulrike Demmer mai magana da yawun Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce Birtaniya za ta ci gaba da kasancewa kawa ga kungiyar ta EU da ma Kungiyar tsaro ta NATO.