Birtaniya ta mika kai akan batun kasafin kudin tarayyar Turai | Labarai | DW | 02.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birtaniya ta mika kai akan batun kasafin kudin tarayyar Turai

Kafofin yada labaru sun rawaito cewar Birtaniya na da shirin bayar da wani kaso na tallafi na musamman da kungiyar EU ke ba ta wanda ake takaddama a kai, don cimma masalaha dangane da batun kasafin kudin kungiyar. Tashar BBC ta rawaito cewa a ranar litinin mai zuwa gwamnatin Birtaniya zata gabatar da na ta tayin bisa manufa ko da yake FM Tony Blair ba ya sa ran cewa za´a soke kudaden tallafin da ake ba manoma. A halin da ake ciki ´ya´yan jam´iyar masu ra´ayin mazan jiya sun zargi Blair da ba da kai ga bukatun kungiyar EU. Jim kadan gabanin haka an jiyo sakataren harkokin wajen Birtaniya Jack Straw na fadawa takwaransa na Jamus Franz-Walter Steinmeier cewa Blair ba ya tunanin rage wani kaso mai yawa na wannan tallafi.