Birtaniya ta amince da ka'idojin EU
December 4, 2017Sai dai a yanzu Birtaniya ta amince da dukkanin sharuda kan iyakoki da take takaddama da makotanta, ciki har da batun sassauci tsakanin ta da lardin Ireland ta Arewa.
A baya Birtaniya ta amince da biyan kudi Euro biliyan 50 a wani yunkuri na mutunta sharuda da EU ta gindaya mata. Sai dai jami'an diplomasiyya na ganin rashin ba da hasken Birtaniyar kan 'yancin 'yan wasu kasashen Turai da ke zaune a kasar, na haifar da kokonto kan makomar cimma matsaya tsakaninta da kungiyar Tarayyar Turai da EU.
A yanzu haka Firaministan Birtaniya Theresa May ta bayyana kyakkayawan fata a tattaunawarta da shugaban majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk, inda take ganin tattaunawar za ta yi tasirin samun damar ci gaba da tattauna batun ficewarta daga kungiyar EU.