1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya: May na kokarin kafa sabuwar gwamnati

Abdullahi Tanko Bala
June 9, 2017

Firaminista Theresa May ta Birtaniya ta nemi gafara daga 'ya'yan jam'iyya mai mulki saboda kiran zaben da ya raunana matsayin jam'iyya da ke rike da madafun iko.

https://p.dw.com/p/2eQll
London Theresa May
Hoto: picture-alliance/empics/D. Lipinski

Firaministar Birtaniya Theresa May ta nemi afuwar yayan jam'iyarta ta Conservative bayan mummunan koma bayan da jam'iyyar ta samu a zaben majalisun dokoki na gaba da wa'adi da ta kira da nufin samun kwarin gwiwar tunkarar kungiyar tarayyar Turai a tattaunawar ficewar Birtaniyar daga kungiyar Tarayyar Turai.

Firaministar ta Birtaniya Theresa May cikin yanayin na bakin ciki da rashin jin dadi ta roki yan  majalisar dokoki na jam'iyyar musamman wadanda suka sha kaye a wannan zabe ta yafe mata. Tana mai cewa ta yi kiran gudanar da zaben domin tana fata game da samun gagarumin rinjaye da zai ba ta damar aiwatar da manufofin da Jam'iyyar ta tsara amma hakan bai samu ba.

Arlene Foster, Parteichefin der nordirischen DUP und Theresa May
Hoto: picture-alliance/empics/C. McQuillan

A yanzu dai bayan da Jam'iyyar Conservative ta gaza samun rinjayen da ta ke bukata a zaben Theresa May ta sanar da cewa ta nemi goyon bayan Jam'iyyar DUP ta Ireland ta arewa domin kafa gwamnatin hadaka.

Tun da farko shugaban jam'iyyar adawa Jeremy Corby ya bukaci Firaministar ta yi murabus kasancewar ta dalilan da suka sa ta kiran gudanar da zaben hakar ta bata cimma ruwa ba. Yana mai cewa a saboda haka ba ta da sauran kima da martaba na ci gaba da jagorancin kasar.

Großbritannien Wahlen 2017 – Jeremy Corbyn
Hoto: picture alliance/PA Wire/D. Lipinski

Ita ma shugabar yankin Scotland kuma jagorar jam'iyyar Scotish National Party SNP Nicola Sturgeon wadda jam'iyyarta ta rasa kujeru a zaben 'yan majalisun dokokin ta soki lamirin Theresa May tana mai cewa SNP ta shiga wannan zabe tare da jan hankali kan jam'iyayar Conservative wadda manufofinta suka haifar da tsadar rayuwa da jefa yara da dama cikin talauci.