Biritaniya zata rage yawan sojin ta a Iraqi | Labarai | DW | 02.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Biritaniya zata rage yawan sojin ta a Iraqi

Faraministan Biritaniya, Mr Godon Brown ya sanar da matakin rage yawan dakarun sojin kasar dake jibge a Iraqi.A cewar Mr Brown,soji dubu ne zasu bar kasar ta Iraqi daga nan izuwa karshen shekarar nan da ake ciki. Mr Brown ya fadi hakan ne jim kadan da kai ziyarar sa ta farko a kasar,tun bayan darewar sa mulki,watanni 7 da suka gabata. Dakarun sojin na Biritaniya dai na jibge ne a garin Basra, don gudanar da aikin kiyaye zaman lafiyar.Nan da watanni biyu masu zuwa ne jami´an tsaron na Iraqi,zasu karbi jan ragamar tafiyar da harkokin tsaro a garin na Basra.A yanzu haka dai akwai sojin kasar ta Biritaniya dubu 5 a kasar ta Iraqi.