1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biritaniya zata kafa sansanin soji a kasar Jibuti

December 22, 2005
https://p.dw.com/p/BvFR

Kasar Djibouti ta amincewa kasar Biritaniya kafa sansanin sojan ta a kasar. Cimma wannan yarjejeniya kuwa ta biyo bayan tattaunawar da ministan tsaron kasar ta Djibouti , wato Ougoureh Kifleh yayi ne da wakilan kasar ta Biritaniya a lokacin ziyarar su ta kwanaki biyu a kasar.

A cewar ministan tsaron na Djibouti za a rattaba hannu amincewa akan wannan yarjejeniyar ne a tsakiyar watan Janairun sabuwar shekara Idan Allah ya kaimu.

Makasudin kafa wannan sansanin soji dai a cewar wakilan na Biritaniya shine taimakawa wajen yaki da aiyukan yan ta´´adda da kuma ta´addanci.

Idan za a iya tunawa kasar Faransa nada bataliyar sojin ta mafi girma a kasar ta Djibouti, ba a da bayan bataliyar sojin Amurka kusan dubu daya da 500 dake kasar.