Biritaniya ta miƙa garin Basra ga sojin Iraƙi | Labarai | DW | 16.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Biritaniya ta miƙa garin Basra ga sojin Iraƙi

Sojin Biritaniya sun miƙa ragamar tafiyar da harkokin tsaro na garin Basra ga sojin Iraqi. Hakan dai zai kawo ƙarshen kasancewar garin Basra ƙarƙashin ikon Biritaniya. Sojin na Biritaniya dai sun shafe a ƙalla shekaru biyar su na gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya a wannan yanki. Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun ce harkokin tsaro a yankin sun inganta. Matakin a cewar bayanai zai kasance babban ƙalubalene ga Gwamnatin Iraƙi a yanzu haka. Rahotanni sun ce bayan miƙa ragamar yankin, sojin Biritaniya dubu biyu da ɗari biyar za su ci gaba da kasancewa a kudancin Iraƙi, ragowar rabin kuma su koma gida Biritaniya.