Binciken take hakkin bil Adama a Dafur | Labarai | DW | 14.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Binciken take hakkin bil Adama a Dafur

default

Sabuwar hukumar kare haƙƙin bil Adama ta Majalisar ɗinkin duniya ta zartar da hukuncin tura tawaga ta musamman zuwa Dafur domin bincikar zargin take hakkin bil Adama da kuma taɓarbarewar halin rayuwar fararen hula a yankin. Hakan na zama wani matakin ƙarin matsin lamba ga sudan ta amince da tura sojin kiyaye zaman lafiya na majalisar ɗinkin duniya domin tabbatar da tsaro da kariyar jamaá a Dafur. A cikin wani sako sakataren majalisar ɗinkin duniya Kofi Annan yace wajibi ne a dakatar da tarzoma da kashe kashen jamaá dake gudana a Dafur.