1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

BINCIKEN MAKARANTUN ISLAMA A A KASAR THAILAND JAMILU SANI:

Yanzua haka dai mahukuntan kasar Thailand sun bada umarnin da a gudanar da bincike a dukanin makarantun musulmi dake kudancin kasar tun a jiya litinin,da nufin ganon mutanen dake da hanun cikin hadarin bomb din da aka dasa makon da gabata wanda kuma yayi sanadiyar lalacewar wasu gine gine tare kuma da mutuwar jami'an tsaron kasar ta Thailand shida.
Ministan cikin gidan kasar ta Thailand Wan Nor ya shaidawa manema labaru cewa,gwamnati nada cikakun rahotanin dake nuna cewa mai yiwa ne wasu yan ta'ada su yi amfani da makarantun kasar a matsayin wani sansanin su,ko kuma maboya da zasu rika amfanin da ita wajen aikata mugan laifuka na ta'adanci.
Priminstan Thailand Thaksin Shinawatra ya nisanta kansa daga rade radin da ake yadawa cewa yayi zargin cewa kungiyoyin musulmi yan ta'ada na amfani da makarantun Islama na kasar wajen horar da aiyukan ta'ada.
Ya dai kara da cewa mafi yawan lokuta alumar kasar Thailand ba kasafai suke tsayawa su fahimci irin yadda kalaman sa suka sa gaba,a mai makon haka sai kwai su rika fadin kalaman da ka iya tada hankalin jama'a mai makon kwantar da shi.
Pm na kasar Thailand ya musanta cewa a ya furta wata kalama a ranar 11 ga wanan wata da muke ciki game da makanarun Islama dake kasar,har ma a ce wani ya ambaci mahukuntan kasar da bada umarnin a gudanar da bincike a makarantun Islamiya na kasar ta Thailand.
Shi kuwa daractan makarantun Islamiya na lardin Pattani Ahmad Kamaewaemusaw,shidawa kamfanin dilancin labaru na APF yayi cewa shugbanin addinin na kasar Thailand sun fito fili suka yi suka zargi Pm kasar da laifin bada umarnin bincika makarantun Islama na kasar,inda suka yin hakan na iya kawo cikas ga harkokin bada ilimi ga daliban kasar ta Thailand.
A chan kuma lardin Narathiwat,mukadashin majalisar koli dake lura da harkokin addinin Islama a kasar ta Thailand Abdul Rosue Aree,nuna rashin jin dadinsa yayi cewa da sanarwar data fito daga bangaren gwamnati cewa,za'a gudanar bincike a wasu makarantun Islama na kasar Thailand.

Abdul Rouse Aree cewa yayi bai wai suna tsoron a bincike makarantun Islama na kasar bane,saboda zargin da gwamnatin ke yi cewa wasu yan ta'ada na amfanin da irin wadanan makarantun wajen aikata aiyuka na ta'adanci,a'a Mabiya addinin Budah na kasar na iya bulo da wasu abubuwan da suka sabawa addinin Islama a kasar.
Tun ranar ranar lahadin data gabata ne dai wasu yan ta'ada suka mamaye wata barikin soji dake lardin Narathiwat kuma suka kashi soji hudu,tare kuma da yin awon gaba da bindigogi 100.
Bayan kwana daya da wanan hari ne kuma tashin wani bomb a garin Panttani yayi sanadiyar mutuwar yan sanda biyu,a lokacin da wadanan yan bindiga dadi suka gudanar da harbe harbe a ofishin yan sanda dake Yala.
Tun dai gwamnati ta zargi wata kungiyar yan sari kanokr ta Mujahedin da laifin kai wadanan hare hare na ta'adanci wasu yankuna na kasar Thailand.
Tun a jiya litinin shuagban hafsan sojin Thailand ya furta cewa jami'an tsaro sun kasa kama wadanan yan ta'ada ko kuma gano inda suka boye makaman da suka sace,a yankin kudancin Thailand mai yawan alumar musulmi,wanda don haka ne Pm kasar ya bada wa'adin nan da mako daya a samo hanyoyin kawo karshe tashen tashen hankulan dake faruwa a kasar.
A yanzu haka dai mahukunta kasar Malaysia sun bada sanarwar kame wasu yan kasar Thailand a arewacin kasar,wanda kuma aka zarga da laifin kai hari wata barikin soji dake Thailnad inda wanan hali yayi sanadiyar mutuwar soji hudu.