Binciken kwamitin Mdd akan Rafik Hariri ya dauki sabon salo | Labarai | DW | 02.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Binciken kwamitin Mdd akan Rafik Hariri ya dauki sabon salo

Kwamitin Mdd dake binciken musabbabin rasuwar tsohon faraministan kasar Lebanon, wato Rafik Hariri, a hukumance ya bukaci tattaunawar ido da ido da shugaban kasar Syria, Bashir Al Asssad da kuma ministan harkokin wajen kasar, wato Farouk Al Sharaa.

Bugu da kari, kakakin wannan kwamiti na Mdd ya kuma shaidar da cewa , kwamitin nasu na kuma son ganawa da tsohon mataimakin shugaban kasar ta Syria, wato Abdul Halin Khaddam nan bada dadewa ba.

Da alama dai bukatar ganawar gaggawar da tsohon mataimakin shugaban kasar ta Syria, nada nasaba da kalaman daya fadi ne cewa, Shugaba Bashir Al Assad ya sha yiwa Rafik Hariri barazana, watanni kadan kafin rasuwar sa.

Tuni dai ministan harkokin wajen kasar ta Syria, Farouk Al Sharaa ya karyata wannan kalami na tsohon shugaban kasar da cewa bashi da tushe balle makama.

Idan dai an tuna, Rafik Hariri ya rasa ran nasa ne bayan da wani bom ya tashi da motar sa a watan fabarairun shekara ta 2005 a can birnin babban birnin kasar ta Lebanon , wato Beirut.