1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Binciken kisan Indiyawa a Jamus

Anan Jamus yan sanda sun nunar da cewa masu raayin rikau ne suka kaiwa wasu yan kasar India takwas hari, a jihar Saxony dake arewacin kasar, a ranar asabar da ta shige.A lokacin da ya kai ziyara a garin Müngen, inda aka aikata wannan danya,kantomar jihar Georg Milbradt yayi allah wadai da wannan hari.Wasu yan kasar India su uku suna kwance asibiti sakamakon harin da gungun mutane hamsin suka kai musu a lokacin da ake bukin baje koli a wannan gari.Indiyawa sun nemi mafaka a wani gidan abinci inda aka yi musu kawanya har sai da yan sanda 70 suka cecesu. Yan sanda biyu da wasu yan kasar Jamus su hudu sun samu raunuka a cikin wannan artabu.Yan sanda sun nemi wadanda suka shedawa idanawarsu, da su taimaka wajen gano masu alhakin wannan aika aika.