1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Binciken kisan Hariri

Minista na shida dake marawa gwamnatin syria baya yayi murabus daga mukaminsa,batu dake dada tsunduma gwamnatin Lebanon cikin rudadi a daidai lokacin da take gudanar da taro ,domin nazarin gyara adangane da gurfanar da wadanda ake zargi da kashe tsohon premiern Syria Rafiq Hariri.Duk da wannan matsala da aka samu ayau din dai,ministocin Lebanon din sun gudanar da taronsu domin amincewa da kudurin mdd na kafa kotun da zata binciki wadanda ake zargi da laifin mkisan gilla wa tsohon premier ,wanda aka zargi jamian gwamnatin syria da abokan huldodinsu na Lebanon.A jiya nedai yan majalisa masu rinjaye dake adawa da da gwamnatin syria,suka gudanar da taro inda dan majalisa Saad Hariri ya gabatar da sanarwa dake bayyana yadda gwamnatin Syria ke hana kokarin kafa kotun da zata bincike kisan gillan na Hariri.