1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Binciken hari kan jiragen ruwan agaji

August 2, 2010

Isra'ila ta amince MƊD ta gudanar da bincike kan harin da ta kai kan jiragen ruwan agaji ga Gaza

https://p.dw.com/p/OaPC
Sauke kayan agaji ga Zirin GazaHoto: AP

Bayan jinkiri na lokaci mai tsawo, a ƙarshe Isra'ila ta amince Majalisar Ɗinkin Duniya ta gudanar da bincike game da harin da sojojin Isra'ilar suka kai kan wani ayarin jiragen ruwan agaji ga Zirin Gaza a ƙarshen watan Mayu. Kakakin gwamnatin Isra'ila a birnin Ƙudus ya ce Firaminista Benyamin Netanyahu ya sanar da babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon wannan labarin. Kawo yanzu Isra'ila ta nuna adawa da kowane bincike na ƙasa da ƙasa dangane da matakan sojin da ta ɗauka. A kuma can birnin New York an jiyo Ban Ki Moon na cewa Firaministan New Zealand Geoffrey Palmer da shugaban Kolombiya mai barin gado Alvaro Uribe za su jagoranci kwamitin binciken. Kwamitin ya kuma ƙunshi wakilan Isra'ila da Turkiya. A ranar 31 ga watan Mayu sojojin ƙundunbalar Isra'ila suka farma jirgin ruwan dake jagorancin ayarin jiragen ruwan kayan agajin inda suka halaka mutane tara dukkansu 'yan ƙasar Turkiya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar