Binciken hari akan jirgin agajin Gaza | Labarai | DW | 09.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Binciken hari akan jirgin agajin Gaza

Isra'ila ta ce ta gargaɗi Turkiyya game da batun kai agaji zuwa Gaza amma ta yi watsi da shi

default

Firaministan Isra'ila Benjamin Natanyahu ya kasance mutumin farkon daya bayar da shaida a gaban hukumar binciken gano abinda ya faru a lokacin harin da mayaƙan Isra'ila suka ƙaddamar akan jirgin ruwan kayan agaji zuwa yankin Gaza na Falasɗinu. Ya ce, kwanaki da dama gabannin ƙaddamar da harin ƙasar Turkiyya ta yi watsi da gargaɗin da Isra'ila ta yi mata da kuma buƙatar data gabatar wa manyan jami'an ƙasar game da batun kai kayan agajin zuwa zirin Gaza. Natanyahu ya kuma furta cewar binciken zai nuna cewar Isra'ila ta ɗauki matakin daya dace ne a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.

Hukumar binciken wadda ke zaman ta a birnin Qudus tana ƙarƙashin jagorancin wani tsohon alƙalin kotun ƙolin Isra'ila ne Jakob Turkei. Mark Regev, kakakin gwamnatin Isra'ila ya yi ƙarin haske akan hukumar:

"Wannan hukumar bincike mai zaman kanta ce. Za su yanke shawarwarin su. A matsayin mu na gwamnati mun gamsu da cewar, mu ne ke da gaskiya, kuma duk wani ingantaccen bincike, zai tabbatar da hakan."

Hukumar binciken dai ta cikin gida ce da Isra'ila ta naɗa, domin gano gaskiyar abinda ya faru a lokacin harin na ranar 31 ga watan Mayu wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Turkawa tara, kana da janyo ɓacin dangantakar diflomasiyya a tsakanin Isra'ila da Turkiyya. Ƙasashen duniya da dama ne kuma suka yi Allah wadai da harin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Mohammed Nasir Awal