1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Binciken burbuɗin tiririn gubar Polonium 210 a birnin Hamburg

Yahaya AhmedDecember 12, 2006

Jami’an tsaro a birnin Hamburg a nan Jamus, waɗanda ke binciken batun guban nan da ta kashe wani tsohon ɗan leƙen asirin Rasha a Birtaniya, sun gano burbuɗin gubar nan Polonium a gidan wasu mutane da ke zaune a birnin, masu kuma alaƙa da tsohon ɗan leƙen asirin. Yahaya Ahmed ya bi mana diddigin yadda ababa ke wakana game da wannan binciken a nan Jamus, ga shi kuma ɗauke da ƙarin bayani.

https://p.dw.com/p/Btx6
Jami'an tsaro a lokacin gudanad da bincikensu a birnin Hamburg.
Jami'an tsaro a lokacin gudanad da bincikensu a birnin Hamburg.Hoto: AP

Jami’an tsaron rukunin ’yan sandan ciki na tarayyar Jamus, sun gano tiririn gubar nan Polonium 210 a binciken da suka gudanar a gidan tsohuwar matar Dimitri Kowtun, wani ɗan ƙasar Rasha da ake zaton yana da hulɗa da tsohon ɗan leƙen asirin Rashan nan Alexander Litwinenko, da aka kashe da guba a birnin London. Farkon sanarwar da jami’an suka bayar ta ce, an gano tiririn ne a kan wata kujera mai faɗi da Dimitri Kowtun ya yi barci a kanta. Har ila yau dai, kakakin jami’an tsaron na HAMBURG, Elmar Lillpopp ta ce sun ƙara gano wani bubuɗin kuma na tiririn gubar. Kamar dai yadda ta bayyanar:-

„A wannan gidan dai, mun sami burbuɗin a ɗakunan barci da na yara. Kazalika kuma, mun gano alamun burbudin gubar a cikin tufafin da aka wanke da waɗanda ba a wanke su ba, da kuma cikin injin wanke tufafi.“

A cikin wata motar haya ma, sai da aka gano burbuɗin tiririn gubar ta Polonium. Hakan dai ya sa masu binciken sun faɗaɗa da’irar bincikensu, inji shugaban rukunin jami’an tsaro na Hamburg, Thomas Menzel:-

„A ran lahadi da ta wuce, mun ba da farkon bayani game da burbuɗin tiririn da muka gano, abin da ya sa muka yi zaton cewa Dimitri Kowtun ne asalinsa. To amma yanzu kuma, mun sami ƙarin bayani, wanda ke nuna cewa ba Dimitri Kowtun ɗin ne ke yaɗa tiririn ba.“

Abin da jami’an tsaron ke zato a halin yanzu dai shi ne, shi Dimitri Kowtun ɗin ne ya kai gubar Polonium ɗin a gidan tsohuwar matarsa. Daga nan ne kuma, tiririn ya sami cuɗanya da wasu mutane, waɗanda su ma suka yaɗa shi. A wani matakin riga kafi da jami’an tsaron suka ɗauka dai, sun kai tsohuwar matar Dimitri Kowtun ɗin da yaranta 3 zuwa asibiti, inda ake binciken halin ƙoshin lafiyarsu.

Har ila yau dai masu binciken ba su samo bakin zaren warware matsalar ba tukuna. Tun farkon watan Nuwamba ne aka rasa inda shi Dimitri Kowtun ɗin yake. Yanzu jami’an tsaron na neman shaidu ne da suka sami hulɗa da shi kafin a rasa bubuɗinsa. Kamar yadda Thomas Menzel ya bayyanar:-

„Muna neman wani direban tasi ne, wanda ya kai Kowtun ɗin a filin jirgin saman Hamburg, inda daga nan ne ya tashi zuwa London.“

A halin da ake ciki dai, ana tuhumar Kowtun ɗin ne da samun hannu wajen shirya kisan da aka yi wa tsohon ɗan leƙen asirin Rashan Alexander Litwinenko, da gubar Polonium 210 a birnin London. Sai dai, har ila yau ba a san inda yake ba. Amma wasu rahotanni masu tushe na nuna cewa, yana kwance a asibiti a birnin Moscow. Mahukuntan Rashan dai ba su tabbatad da hakan ko kuma yi inkarinsa ba.