1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Binciken ƙunshin kaya mai ɗauke da bom

October 31, 2010

Hukumommin ƙasar Yaman na ci da farautar masu saƙon wani ƙunshi da ke ɗauke da bom, zuwa Amirka

https://p.dw.com/p/Pv8E
Hoton wani abu mai kama da bom da aka gano a cikin ƙunshin kayaHoto: AP

Hukumomin ƙasar Yaman na ci gaba da farautar waɗanda suka aike da ƙunshin sako mai ɗauke da bom a cikinsa da aka aike ta wasu jiragen sama guda biyu zuwa ƙasar Amirka wanda ya ta da fargaba a fannin daƙon kaya ta jiragen sama a duniya baki ɗaya. A jiya Asabar hukumom sun cafke wata mata game da zargin yunƙurin na Al-Ƙa'ida. Jami'an Yaman sun ce an bi diddigin matar ne ta lambar wayar tarho da aka rubuta a jikin rasidin ƙunshin kayan da aka samu a jiragen daƙon kaya da suka sauka a Birtaniya da Dubai a ranar Juma'a. Kafofin yaɗa labarai a Dubai sun ce hukumomi a ƙasar sun ƙaddamar da gagarumin binciken wasu da ake zargi suna da dangantaka da reshen al-Ƙa'ida a Yaman. A yanzu dai ƙasashe da dama sun tsaurara matakan tsaro akan kayayyakin da aka shigo da su ta jiragen daƙon kaya, yayin da firaministan Birtaniya, David cameron ya ce bom ɗin da aka samu a ƙunshin kaya a ƙasar, an yi ne da niyyar tarwatsa jirgin. Ƙasashen Jamus da Faransa kuma sun ce sun daina karɓar jiragen daƙon kaya daga Yaman.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala

Edita: Halima Balaraba Abbas