Bincike a yunkurin juyin mulki a kasar Liberia. | Labarai | DW | 13.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bincike a yunkurin juyin mulki a kasar Liberia.

Gwamnati kasar Liberia ta bada sanarwar buda bincike, domin gano gaskiyar magana, a game da, rundamin juyin mulki, da a ka zargi wasu sosjoji da shiryawa, kwanaki kadan bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasa.

Magoyan bayan dan takara da sha kasa a wannan zabe wato Gerorges Weayah na ci gaba da shelar an tabka magudi ga zaben.

A kwanaki 2 jerai jerai, su na gudanar da zanga zanga a Monrovia babban birnin kasar.

Ministan watsa labarai, da ya hido sanarwar fara binciken, ya ce akwai ministoci 2 ,da ke da hannu a cikin yunkuri juyin mulkin, saidai bai bayyana sunayen su ba.

A nasa bangare Georges Weayah a wata hira da yayi da gidan redion King mallakar sa, ya zargi jami´an tsaro da cin zarafin magoya bayan sa a saklamakonarangamar da su ka yi ranar jiya, ya kuma yi watsi da zargin da jami´an tsaro ke masa, na shirya juyin mulkin.

Ministan tsaro na kasar Liberia da shima masu zanga zangar su ka abkawa motar sa, ya tabatar da daukar matakan gurfanar da dukan wanda a ka samu da hannu a cikin lalata dukiyar jama´a a zanga zangar da magoya bayan Georges Weayah su ka shirya.