1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bincike a game da harin da ya rutsa da Guillaume Sorro

July 12, 2007
https://p.dw.com/p/BuGY

Gwamnatin ƙasar Cote D´Ivoire ta yanke shawara danƙawa Majalisar Ɗinkin Dunia yaunin bincike, a game da harin da ya rutsa da Praminista Guillaume Soro, ranar 29 ga watan da ya gabata, a birnin Bouake cibiyar tsafin yan tawayen FN.

A jiya ne shugaban ƙasa Lauran Bagbo, ya jagoranci taron mussamman, na majalisar ministoci, wanda ya yanke wannan ƙuduri.

Idan dai ba a manta ba, wasu mutane ne,ɗauke da manyan makamai, su ka abkawa jirigin da ke ɗauke da Praministan Guillaume Soro, minti ɗaya bayan saukar sa, a filin saukar jiragen samar Bouake ranar 29 ga watan Juni da ya wuce.

Ya zuwa yanzu kuma, ba a tantance ko suwa ke da alhakin kai harin ba.

Wannan al´amari, ya hadasa saban ruɗami a ƙasar Cote D´Ivoire bayan yarjejeniyar sulhu da aka cimma tsakanin yan tawaye da dakarun gwamnati.