Bin diddigin 'yan Najeriya masu fataucin 'yan Adam
Wakilan DW Jan-Philipp Scholz da Adrian Kriesch sun bi sawu mai hatsari na masu fataucin 'yan Adam daga Najeriya zuwa Italiya. Sun gano yadda aka mayar da mata matasa 'yan Najeriya tamkar bayi suna karuwanci.
Guje wa talauci
Mun fara binciken ne a Bini, helkwatar jihar Edo. Kusan duk wanda muka zanta da shi yana da aboki ko dan uwa a Turai. Sama da kashi uku bisa hudu na masu aikin karuwanci ba bisa ka'ida ba a Italiya sun fito ne daga jihar. Saboda rashin aikin yi tsakanin matasan Edo, daukacin mata matasa ba sa hangen wata makoma a jihar. Suna neman kyakkyawwar rayuwa a Turai ba tare da sanin hadarin da ke ciki ba.
Alkawura na karya
Sista Bibiana Emenaha ta Katholika ta shafe shekaru tana kokarin gargadin mata matasan Najeriya kafin su karasa Turai. "Ana yaudararsu da alkawura na bogi," inji ta. Masu fataucin suna alkawarta musu sama musu aikin yi na reno yara ko gyaran gashi, amma duk a karya. Da zarar matan matasa sun isa Turai, suna karewa ne kan tituna suna aikin karuwanci.
"Muntanen mahandama ne"
Bayan wata doguwar tattaunawa, wani dan sumoga ya yarda ya yi hira da mu. Ya kira kansa Steve kuma ya yi ikirarin kai matan Najeriya fiye da 100 zuwa kasar Libya. Bai yi magana game da wadanda suke wannan harkar tare da shi ba. Ya ce shi dan hidima ne kawai. "Mutane a nan jihar Edo manhandama ne. A shirye suke su yi ko mene ne don samun rayuwa mai inganci," inji Steve.
Tafiya mai hatsari cikin Sahara
Steve na karbar Euro 600 ($666) mutum daya a tafiyar daga Najeriya zuwa Libya. "Mafi yawan mutanen sun san yadda tafiya cikin Sahara ke da hatsari," inji mai fataucin 'yan Adam. Mutane da yawa na mutuwa kan hanya. "Wannan ita ce kasadar," inji Steve, wanda da kanshi ne yake kai bakin hauren Agadez a Nijar. Daga can abokinsa ya karbi ragama.
Agadez: Tungar masu fataucin 'yan Adam
Garin Agadez da ke cikin hamada, shi ne wani bangare mafi hatsari a binkenmu. Garin na cin amfani daga fataucin 'yan Adam da kwayoyi, sannan akan yi garkuwa da baki don neman kudin fansa. Sanye da rawani da ya rufe fuskokinmu kuma tare da masu tsaron lafiya dauke da makamai ne muka iya yawatawa cikin garin.
Magance matsalar kaura
Kamar da yawa na mazauna garin da ke cikin hamada, shi ma Sarkin Agadez Omar Ibrahim Omar, na ganin fataucin 'yan Adam matsala ce da ba za a iya magance ta a Agadez ba. Ya nemi kasashen duniya sun taimaka da karin kudi. Hujjarsa: Idan Turai ba ta son bakin haure su rika bi ta Tekun Bahar Rum zuwa nahiyar, to ta kara yawan taimakon da take ba wa Nijar.
"Ayarin Motocin ranar Litinin" zuwa Libya
Tun wasu watanni ke nan ayarin manyan motoci dauke da bakin haure suke tashi daga Agadez zuwa arewa ko wace ranar Litinin kafin faduwar rana. Rikicin kasar Libya ya taimaka masu fataucin 'yan Adam na iya kaiwa bakin Tekun Bahar Rum ba da wani bincike da aka saba a da ba. Nan da nan mun gano cewa hukumomi a Nijar ba su damu sosai da aiyukan masu fataucin ba.
"Yawan 'yan mata masu karancin shekaru"
Da yawa daga cikin bakin daga Najeriya suna karewa kan titunan Italiya. Ma'aikaciyar jin dadin jama'a Lisa Bertini na aiki da karuwai daga kasashen waje. "Yawansu na karuwa," inji ta. Alkalumman hukuma sun ce kimanin 'yan Najeriya dubu daya ne suka shiga Italiya ta Bahar Rum a 2014. A 2015 alkalumman sun haura zuwa dubu hudu."Yawan 'yan mata masu karancin shekaru na karuwa," inji Bertini.
Neman "Madam" wato magajiya
Da taimakon abokin aiki daga Najeriaya, mun gano wata da ke zama "Magajiya" a arewacin Italiya. Ana kiran 'yar Najeriya mai masaukin baki "Madam" tana kololuwar wani gungun 'yan fautauci. "Madam" din da muka gano na zaune a wata unguwa da ke wajen birnin Florence. Wata ta zargeta da kakkausan lafazi: "Tana dukanmu tana kuma matsa mana mu yi karuwanci, inji wadda aka ci zalinta.
"Madam" dan 'yan matanta
Da muka tinkari "Madam" din game da zarge-zargen da aka yi mata, ta amsa cewa ta ba wa mata matasa 'yan Najeriya su shida masauki a gidanta, amma ta musanta tilasta musu shiga karuwanci. "Abin da matasa 'yan Najeriya a nan ke yi ke nan." Bayan hirarmu mun mika sakamakon bincikenmu ga ofishin mai gabatar da kara na Italiya.
Rashin katabus daga mahukunta
Sista Monika Uchikwe ta dade tana sukar mahukuntan Italiya da rashin wani katabus. Shekaru takwas ke nan tana kula da wadanda ta'asar fataucin ta shafa. Ta fusata lokacin da muka muka yi mata tambaya game da kwastamomi. A kullum mazan na son su samu gamsuwa cikin sauki da araha- Euro 10 ne yin jima'i da 'yar Najeriya da ke gilo kan titi. "Wannan ke sa matsalar ke ci gaba da wanzuwa," inji ta.